Scotland ta amince da mata Musulmai ‘yan sanda su dinga saka hijabi a wajen aiki


 

 

Gwamnatin kasar Scotland ta amincewa mata Musulmai ‘yan sanda da su dinga saka hijabi a yayin gudanar da aiyukansu.

Wannan mataki ya biyo bayan kokarin gwamnatin na kara yawan mata ‘yan sanda Musulmai a kasar.

Shugaban Rundunar ‘Yan sandan Scotland Phil Gormley ya ce, ya yi matukar farin cikji da wannan sanarwa da ya bayar. Kuma suna son ganin Musulmai a aiyukan ‘yan sanda kamar yadda suke a sauran bangarorin aiyukan gwamnati a kasar.

Kungiyar ‘Yan sanda Musulmai ta Scotland ta ce, wannan mataki zai taimaka waje sake hada kan al’umar kasar.

Shugaban Kungiyar Fahad Bashir ya ce, suna tunanin wannan mataki ya yi kyau kuma suna maraba da shi.

Ya ce, shekaru 15 kenan a kasar ba a ba wa kananan ‘yan sanda damar saka hijabi a Scotland amma yanzu an samu wannan dama.

A dokar shekarar 2001 da ta samar da kayan ‘yan sandan kasar an tanadi hijabi a cikinta.

You may also like