
Asalin hoton, OTHER
A Sfaniya kungiyar kwallon kafa ta Sevilla ta cimma matsaya da Isco, inda duka bangarorin biyu suka aminta a kawo karshen zamansa.
Tsohon dan wasan na Real Madrid ya koma Sevilla ne cikin watan Agusta, inda suka kulla yarjejeniyar shekara biyu.
Bayan zuwa Madrid daga Malaga a 2013, Isco ya taimaka wa Real lashe kofunan zakarun Turai biyar da na La Liga uku.
To amma yanzu Sevilla ta yanke shawarar soke yarjejeniyar da ta kulla da dan wasan na Sfaniya.
Akwai rahotannin da ke cewa kocin kungiyar ne Jorge Sampaoli ya nuna bai da sha’awar saka shi cikin jerin yan wasan da za su buga masa wasanni.
An kuma ce ya yi fada da daraktan wasannin kungiyar Monchi, yayin atisaye watan da ya gabata.
Isco ya ci wa Sfaniya kwallaye 12 a wasa 38, kuma tun a 2019 bai sake saka mata riga ba.