Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta ayyana Seyi Makinde na Jam’iyyar PDP a matsayin ɗan takarar da ya lashe zaɓen gwamna a jihar Oyo a zaɓen ranar Asabar da aka gudanar.
Makinde wanda shi ne gwamna mai ci a jihar ta Oyo ya samu ƙuri’u mafi yawa inda ya bai wa babban ɗan adawa a jihar, Teslim Folarin na Jam’iyyar APC tazarar ƙuri’u dubu 300.
INEC ta ce Seyi Makinde ya samu ƙuri’u 563,756 yayin da Teslim Folarin na APC ya samu ƙuri’u 256,685.