An kaiwa sojojin Mogadishu babban birnin kasar Somaliya harin ban inda aka kashe mutane takwas.
Kungiyar ta’adda ta Al-Shabab masu alaka da ‘yan Al-Qaeda ne suka doki alhakin harin.
Kungiyar ta’adda ta Al-Shabab na kokarin ganin sun kafa daular Islama a kasar. Wannan shi ne daliln da ya sa a kowanne lokaci suke kai hare-haren bama-bamai a Mogadishu babban birnin kasar.