
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Joe Biden
Jawabin da shugaban Amurka ke yi na shekara-shekara na shekarar 2023 ya zo da ƙalubale saboda matsalar da ya daɗe yana fuskanta musamman a lokacin yin jawabi a bainar jama’a.
Sai dai ba shi kaɗai ba ne, domin akwai wasu sanannun mutanen da suka daɗe suna neman yadda za su shawo kan matsalar.
Jawabin da shugaban Amurka ke yi wa ‘yan kasar a kowace shekara daga zauren majalisar kasar abu ne mai sarkakiya ga dukkan shugaba, domin ana sa ran zai gabatar da jawabi mai ratsa zuciya. Sai dai wannan gagarumin aiki ne ga Joe Biden.
Shugaban ya dade yana fama da matsalar in’ina tun farkon rayuwarsa ta siyasa. Amma in’in ba mutane kalilan kawai ta shafa ba – an kiyasta akwai kimanin mutum miliyan 80 a fadin duniya – wato mutum daya cikin mutum 100 – da ke fama da in’ina.
Akwai kuma kashi daya cikin 20 na mutanen da tun suna kananan yara suke fama da matsalar ta in’ina.
Wannan na nufin ba abin mamaki ba ne a ci karo da fitattun mutanen da ke yin in’ina. Sai dai abin lura shi ne wadannan mutanen a su cika son bayyana halin da suke cika ga kowa ba.
Jajircewar da Biden ke yi
A misali, Mista Biden ne shugaban Amurka na farko da aka fito fili aka ce yana da in’ina yayin da yake jagorantar kasar.
Wannan ya biyo bayan rahotannin da ke cewa wasu shugabannin da ya gada kamar Thomas Jefferson da Abraham Lincoln, wadanda suka rayu cikin karni na 18 da na 19 su ma sun yi fama da matsalar.
Amma shugaban mai-ci bai boye nasa matsalar ba, musamman ma a lokacin da suka yi wata zazzafar muhawara da tsohon shugaba Trump a 2020.
Biden ya ce, “In’ina ita ce matsalar da idan ka yi tunani, ta kasance lalurar da har yanzu jama’a ke yi wa mai ita dariya, su kan tozarta mai yin ta”.
Yin ashar domin samun ‘waraka’ daga in’ina
Tauraron fina-fina Hollywood din nan Samuel L Jackson ya shahara sosai kan yawan rawar da ya taka a fim, ya kuma shahara kan yawan lokutan da ya rika furta kalaman zagi – ya taba kafa tarihin yin ashariya har sau 40 cikin fim daya kacal.
“Tun ina karami nake da matsalar in’ina, kuma yin ashar ya taimaka min kawo karshen matsalar. Yin haka ya bani wata damar mayar da hankali kan wani abin na daban wanda ya bani damar samun waraka,” inji shararren dan fim din yayin wata hira da yayi da mujallar Vanity Fair a 2019.
“Ban san dalili ba, amma kalaman zagin da nake ambata a fina-finai na da saukin fadi a gareni. Har zuwa yau kalmomin na taimako na.”
Amma baya ga yin ashariya, Jackson na yin ‘atisayen’ numfashi domin taimaka wa kansa rabuwa da lalurar.
Shi kuwa fitaccen dan wasan Golf din nan Tiger Woods ya gano wata hanyar kauce wa matsalar ne: ya rika gwada yin jawabai ta hanyar tattaunawa da karensa.
“Nakan rika yin magana da karena, shi kuma sai ya zauna yana sauraren abin da nake cewa har barci ya dauke shi”, inji Woods cikin wata hirar da yayi da tashar talabijin ta CBS ta Amurka a 2006.
“Daga nan ne na gano yadda zan yi jawabai ba tare da na rika yin in’ina a koda-yaushe ba.”
Matsalar ta fi shafan maza kan mata
Kungiyar masu lalurar in’ina ta Amurka ta ce matsalar ta fi shafar maza, musamma idan aka duba lalurar tsakanin kananan yara. Masana kiwon lafiya sun kasa gano abin da ke sa maza suka fi mata samun wannan lalurar.
Wata mata da ta fito fili ta bayyana halin da in’ina ta saka ta ita ce Emily Blunt, wata tauraruwar fim ‘yar Birtaniya. A 2020, ta tattauna kan batun yayin wata hira da ta yi da mujallar Marie Claire ta masu tallata kayan kawa, inda ta ce ta fada tsundum cikin matsalar yayin da take tasowa a birnin Landan.
Ta ce sai bayan da ta fara koyon wasannin kwaikwayo ne ta gano cewa idan ta sauya salon magana zuwa karin bakin da ba nata ne ba, sai kawai lalurar ta bace nan take.
“Mayar da kaina wata mace daban da ainihin matar da nake ya ‘yantar da ni. Na rika yin magana da karin harshen mutanen arewacin Ingila, amma sai na gano ashe hanya ce ta samun waraka daga in’ina.” Blunt ta ce a duk lokacin da ta kwaikwayi karin harshen wata al’ummar, sai ta ga ba ta in’ina.
A karshe akwai mawaki Ed Sheeran
Wannan marubi kuma mawakin ya sami shahara ne ta hanyar tsayawa a gaban masu sauraron wakokinsa shi kadai yana dauke da da garayarsa, abin da ke razana yawancin mawaka ko da ba su da in’ina.
Amma tun farko Sheeran ya gano hanyar yin amfani da wasu baituka daga wakokin dan gambarar nan Eminem – domin ya hana shi razana yayin da yake yin jawabi ko yin wakoki.
“Mahaifina ya sayo min wasu daga cikin wakokinsa yayin da nake da shekara tara da haihuwa,” inji mawakin yayin wani jawabi da yayi a cibiyar bincike kan in’ina ta Amurka a 2015.
“Na koyi dukkan kalmomin da ke cikin kundin wakokin. Eminen na da saurin magana yiyin da yake wakarsa ta gambara. Hakan ya taimake ni rabuwa da in’ina.”