Shan Magunguna Ba Tare Da Umarnin Likita Ba Na Hana Haihuwa 


Hoto:The Cable

Rashin haihuwa na kara yawa a kasashen Afirika saboda yadda ake yawan shan maganin da ba Likita bane ya umarci mutum yasha ba hakan yana shafar gabobin da suke kula da haihuwa. 

Wata kwararriya likita mai suna  Ifeoma  Amugo dake aiki da majami’ar Redeemed Christian Church of God(RCCG),ta bayyana haka. 

Amugo ta bayyana hakane a wurin taron mata da majami’ar ta gudanar a Abuja.

 A cewar ta ana samun karancin haihuwa  a kasashen Afirika fiye da kasashen nahiyar Turai, saboda a kasashen da sukaci gaba ba a siyar da magani a kanti ba tare da takardar dake nuni da umarnin Likita ba.

 Tace wasu mata sun lalata mahaifarsu da kuma kwayayen haihuwarsu saboda illar magungunan da suka rika sha a baya.  


Like it? Share with your friends!

0

You may also like