Shanu 11,571 Aka Sace Cikin Watanni Uku A Jihar Kaduna 


Wata kungiyar Fulani da ake kira GAFDAN , tace sama da shanu 11,571 aka sace a kananan hukumomin hudu dake jihar Kaduna,a cikin watanni uku. 

Sakataren kungiyar,  Bature Daji ya bayyana haka ga manema labarai, a garin Kaduna, yace kananan hukumomin da abin yafaru sun hada da Chi.kun,Kajuru,Kachia da kuma Igabi.

“Masu satar shanu suna yawo da manyan bindigogi,saboda haka babu yadda za’ayi mai shanu ya iya tunkararsu”yace

Yace barayin shanun sun kashe Fulani da dama a gidajensu da kuma wuraren kiwi. 

Daji yayi kira ga gwamnatin jihar da takawo musu dauki, inda yace a shirye kungiyar take data bawa jami’an tsaro hadin Kai. 

Yace barayin shanun sun fito ne daga kabilu daban-daban ,tare da hadin kan matasan Fulani ayin satar. 

“Damuwar mu ba wai ta kabilar da suka fito bace, a’a damuwar itace dukansu yan ta’adda ne da yakamata ace an ganosu, anyi kuma maganinsu,” yace. 

You may also like