Shanu Sun Hana Jirgi Sauka a Filin Saukar Jiragen Sama a Jahar Imo


 

Jim kadan kafin jirgin ya sauka ne matukin jirgin ya fuskanci cewa shanu sun mamaye wajen da jirgin zai sauka, al’amarin da ya sanya shi ya sauya hanya, ya jinkirta har sai da jami’an tsaro suka kai masu dauki wajen korar shanun.

Wannan al’amari ya faru ne a filin saukar jiragen sama na Sam Mbakwe da ke Owerri, a jahar Imo a jiya Alhamis.

Fasinjojin da ke cikin jirgin har sun tsure suna tunanin ko da gangan matukin jirgin ya karkatar da jirgin. Sai da daga baya suka fahimci abunda ke faruwa.

Wannan ba shi ne karo na farko da shanu ke mamaye filin saukar jirgi ba a Nijeriya. Akwai lokacin da wani jirgin Air France ya yi ciki da shanu a filin saukar jjiragen sama na garin fatakwal, al’amarin da ya ruda fasinjojin, ya kuma haifarwa da jirgin matsala.

You may also like