Wasa-wasa daga shiga shekarar 2022 ga shi har an fara bankwana da ita.
Sai dai kamar kowace shekara, ita ma ba ta yarda ta tafi ba tare da barin wani abu da za a dinga tunawa da ita ba.
Kama daga kan daɗi da wuya kamar yadda suke a halayyar yau da gobe, har zuwa kan sara ta amfani da wasu kalmomi da suka yi tashe.
Wasu kalmomin daga waƙoƙi aka samo su, wasu kuma da wahala a samu wanda zai bugi ƙirji ya ce ga salsalarsu.
Ko ma dai mene ne, to an wataya da yayin su a tsakanin masu magana da Hausa a Najeriya.
Bari mu ɗan tuno wasu daga cikinsu.
Asalin hoton, Presidency
Sharholiya
Duk da cewa sai a wajen watan Nuwamba aka fara yayin kalmar ka’in da na’in bayan hirar Shugaba Muhammadu da gidan talbajin na Tambati ran 30 ga watan Oktoba, amma sai da ta fi kowace kalma shahara a 2022.
Tambayar Shugaba Buhari aka yi a hirar cewa me ya sa yake yawan jaddada batun za a gudanar sahihin zabe a Najeriya.
Sai ya amasa cewa: “Ai wannan ya kamata a ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.
“Dubi zaɓen da aka yi a Anambra da Ekiti da Osun (wato yana nuni da cewa sahihan zaɓuka ne).
“Zan tunawa ‘yan Najeriya da yake su sharholiya ta yi musu yawa, abin da kawai suka ga dama suke magana a kai, ba a tsayawa a yi zurfin tunani.”
Ai ko shi kenan aka samu sarar sharholiya. Kuma ma dai ga alama an yi sharholiya iya sharholiya bana.
Vawulence
Duk da cewa wannan kalmar Turanci ce, amma ba ƙaramin tashe ta yi ba a tsakanin dukkan ƴan Najeriya ciki har da masu magana da Hausa.
Ainihin kalmar dai ana rubuta ta ne kamar haka, “violene”, wato rikici kenan.
Sai dai har a rubuce da yadda ake faɗar ma sai da aka sauya.
Tun shiga 2022 abu kaɗan mutum ya yi sai ka ji an ce masa “kai irin wannan Vawulence haka!,” ko kuma a ce “Vawulence pro-max” wato dai vawulence din ma mataki-mataki ne.
Bari mu gani ko Vawulence za ta ci gaba har gaba da 2022.
Abin ya motsa
Abin da ya sa na yi waƙar ‘Abin ya motsa’
Da jin kalmar sai ka yi tsammanin ko wani ciwon hauka ko na hassada ne ya motsa ko?
To wannan karon dai ciwon so ne ya motsawa Sadeeq Saleh, wani sabon mawaƙi a cikin waƙarsa ta soyayya da ya saka wa suna “Abin ya motsa” ɗin.
Cikakken baitin amshin waƙar ma cewa ake “Abin ya motsa, yana dukan rai, ya bakin ganga, soyayya ce.”
Kan kace kwabo sunan waƙar ya zama sara, ta yadda mutane ke lanƙaya shi ba ga soyayya ba kawai har ma ga sauran al’amuran rayuwa.
Ko shirme mutum ya tafka sai a zolaye shi da cewa “to fa, abin ya motsa.”
To 2022 dai ta mommatsa, Allah Ya kai mu 2023 da rai da lafiya mu ga me zai motsa.
Pie/Ta fashe
Kai jama’a, bana ƴan Pi sun sha jira a duniyar nan ta Maliki Yaumuddini.
Tun watan Disamban 2021 ake ana sa ran za ta fashe, don dubban mutane ma har sun sha alwashin za su ci karensu babu babbaka a watan Janairun 2022, har sai da manda ya fara fita daga kan kaza.
Yau ne, gobe ne, Pie dai shiru kake ji har 2022 na neman ƙarewa ba ta fashe ba, sai dai kalmomin biyu da na pie da ta fashe sun yi matuƙar tashen da zai yi wahala idan akwai waɗanda suka kai su.
To ‘yan pie dai da yawa har yanzu suna nan suna jiran tsammani, don kuwa ba su fitar da rai ba kamar yadda suka ce, wataƙila su dace a sabuwar shekarar 2023.
Kwamared
Wai da suna yana ƙarewa da tuni na Kwamared ya ƙare a shekarar 2022.
Kwamared dai, Kwamared dai, wannan bawan Allah ya sha kira, iya kira.
Kwamared dai na nufin ɗan gwagwarmaya ko ɗan kishin ƙasa, amma sai ga shi a 2022 sunan Kwamared ya ɗauki wata sabuwar ma’ana.
Yanzu da an ce wa mutum Kwamared to ana nufin “ɗan ƙanƙamo, ba kuɗi sai Turanci, mai ɗaukar wanka, wanda a ganinsa ya fi kowa wayewa, wata rana ma har da kum yake yawo maƙale a jikin sumarsa.”
An daɗe ba a cashewa wani ba kamar yadda aka cashewa Kwamared, musamman a tsakiyar shekarar nan.
Har sai da ta kai wa wasu Kwamarawan suka dinga yakice laƙanin Kwamared din da ke lanƙwaye da sunayensu da a baya har tunƙaho suke da shi.
Allah dai ya bar girma Kwamarawa.
Besty/Cousin
Ƙarshen vawulence da aka yi a 2022 kenan, wato yayin batun Besty da Cousin.
Besty dai ana nufin namiji babban abokin wata budurwa mace, cousin kuma yana nufin ɗan uwanta da ake kira abokin wasa a Hausa.
Su waɗannan rukunin mutane sun ga ta kansu a bana, inda aka dinga zolayarsu ana bayyana su a matsayin su ne suka fi hatsari ga duk saurayin da budurwarsa ko angon da amaryarsa ke da besty ko cousin.
A wasu muhallan ma dai a taƙaice kallon “kwarto” ake yi musu.
Warr/Cass
Asalin hoton, Ado Gwanja Facebook
Fitaccen mawaƙin Hausa ma Ado Gwanja sarar kalmomi biyu ya kawo a cikin wasu sababbin waƙoƙinsa na bana.
“Warr, ku yi ta kanku, mu ma mu yi ta kanmu, dariya ba fa so ba.”
To wannan kalma ta Warr aka dinga warwarewa mutane ita. Ta zama tana ɗaukar ma’anoni da yawa.
Warr ba ta yi sanyi ba sai ga Ado da Cass kuma.
Ita ma dai wannan kalma an same ta ne a cikin wata sabuwar waƙarsa.
Da alama dai Warr da Cass sun zauna a bakin mutane daram.
Kebura
Asalin hoton, Fati Slow Facebook
Duk lokacin da na ji an ce kebura sai Fati Slow ta faɗo min a rai.
Wata tsohuwar ƴar fim din Hausa Fatima Usman da a yanzu aka fi sani da Slow ce ta fara ba da sarar kalmar, wataƙila ba don ta yi tashe ta faɗe ta ba, amma sai ga shi ta zama ruwan dare.
Wata cakwakiya ce ta kunno kai a Kannywood a kan yawan kuɗaɗen da ake biyansu, bayan wata hira da BBC ta yi da Hajiya Ladin Cima, Tambaya.
A hirar dai Tambaya ta ce abin da ake biyanta a fim ba ya gaza naira 2,000, lamarin da ya sa aka yi ta sa’insa har Fati Slow ta shiga zancen inda ta wanke Sarkin Waka Naziru kan goyon bayan Tambaya da ya yi, da ƙin goyon bayan su Ali Nuhu da batun ya tunzura.
Sai dai kwatsam bayan ƴan kwanaki sai ga Fati ta canza magana inda ta fito tana yabon Sarkin Waka.
Yaya aka yi haka ta faru? Sai ta ce ai Naziru ya wanke ta ne tas da ruwan naira, “ya cire mata kebura 99,” wato ma’ana ya cire mata rigar talaucin da ta yi mata dabaibayi.
Shi kenan kuwa aka samu sarar kebura.
Olule in ji Tinubu
Duk da kasancewarsa ba Bahaushe ba, amma sai da ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya bar wa Hausawa sarar wata kalma a 2022 da zai yi wahala ta shuɗe daga tarihi.
Wannan kalma dai ita ce “Olule” wato faɗuwa kenan.
A wani taro da aka yi a wata jiha da ke yankin Kudu Maso Yamma ne kafin zaɓen fitar da gwani na APC, aka jiyo Tinubun yana bayani na gugar zana cikin Yarbanci.
A kaikaice ya yi ta jefa wa Shugaba Buhari baƙar magana ne na kan yadda ya taimake shi ya ci zaɓe, don haka shi ma lokaci ya yi da zai ramawa kura aniyarta.
Asalin hoton, Bola Tinubu Facebook
A jawabin ya ce: “Oshegini olule, oshegeji olule, oshegeta olule.” Ma’ana “Ya faɗi a karo na farko, ya fadi a karo na biyu, sannan ya faɗi a karo na uku.”
Tab! Aiki ga mai ƙare ka, ai kuwa ya bai wa ƴan Najeriya aiki musamman ma Hausawa, duk da cewa ba da yarensu aka faɗa ba.
Yanzu kalmar Olule har ta zama jiki ga mutane.
Jikin ta ƙaura ya yi la’asar
Bari na ƙarƙare da kalmar Jikin ta kaura ya yi la’asar, don ni ɗin ma na yi lis da rubutu.
Duk da dai ba a shekarar 2022 aka fara amfani da kalmar ba, amma ta yi tsirin tashe a bana.
Wato ana nufin idan jikin mutum ya yi sanyi kenan, sai a ce ai jikin ta ƙaura ya yi la’asar.
Allah Ya sa mu ga shekarar 2023 cikin ƙoshin lafiya da ƙaruwar arziki da imani da wadata.