Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya karyata zargin da ake masa cewa ya karbi dala miliyan 200 a matsayin cin hanci daga manyan kamfanonin mai na Shell da ENI, sakamakon cinikin wata rijiyar mai a gabar teku da ke yankin Naija Delta a kasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban, Ikechukwu Eze, ya fitar, ya ce wadannan zarge-zarge duk ‘labaran bogi ne’, wadanda aka kirkiro da nufin bata sunan Mista Jonathan a idon kasashen duniya.
Mista Jonathan ya ce bai san tsohon ministan mai na kasar Dan Etete ba, wanda shi ne ya kitsa wannan yarjejeniya mai cike da rudani, ya kuma karbi makudan kudi daga kamfanin Shell a cinikin wannan rijiyar mai, wadda aka ce mallakinsa ce.
Sai dai a cewar ma’aikatan Shell a wani rahoto, sun yi ikirarin cewa Mista Jonathan da Mista Etete sun san juna tsawon shekaru, tun lokacin da Mista Jonathan ya koyar da ‘ya’yan Mista Etete lokacin yana ministan mai.