A halin yanzu, Karamin Kwamitin kawo karshen rikicin Fulani da manoma da Mataimakin Shugaba Kasa, Yemi Osibanjo ya kafa a karkashin jagorancin Gwamnan jihar Ebonyi ya yi zama har sau biyu inda ya kuma fara bayar da wasu shawarwari da za a fara bi wajen kawo karshen wannan rikicin kamar haka:
> Kwamitin ya nemi a hada rundunar hadin guiwa ta sojoji da ‘yan sanda wadanda za su rika murkushe wani kazamin rikici da ya taso tsakanin bangarorin biyu idan har bukatar haka ta taso.
> Kwamitin ya nemi a karfafa harkar leken asiri a yankunan da ke fama da rikice rikicen.
> Kwamitin ya nemi amfani da karfin soja wajen murkushe barayin Shanu wadanda ke da hannu a cikin rikicin a fakaice.
> Kwamitin ya nemi a saka sarakunan gargajiya cikin duk wani sulhu da za a yi a yankunansu.
> kwamitin ya nemi a horas da rundunar kula da gandun daji wadanda za su rika kula da tsaron yankunan da aka kebewa makiyaya don kiwon dabbobinsu da kuma burtulolonsu.
*
Ko kuna da wasu shawarwari da kuke ganin za su taimaka wajen shawo kan wannan matsala na rikicin Fulani da manoma wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane d dama?