Sheikh Abdul Aziz na fama da rashin lafiya


 

 

Babban Muftin kasar Saudiyya Sheikh Abdul Aziz ba zai yi wa mahajjatan shekarar bana huduba a tsaye ba, sabili da halin rashin lafiya da yake ciki.

Kafar yada labarai ta AFP ce ta rawaito wannan labarin.

Tsawon shekaru 35 da ya yi yana rike da wannan mukamin,wannan shi ne karo na farko da Muftin zai yi wa mahajjata huduma a zaune daga masallacin Namira da ke a gaf da dutsen Arafat,.

Sheikh Abdul Aziz dai ya maye gurbin magabacinsa Sheikh Abdel Aziz bin Baz wanda ya kwanta dama a shekarar 1999.

A cikin hudubarsa ta shekarar bara,shehin malamin ya tabo batun ‘yan ta’adda da kuma ‘yan tawaye nkasar Yaman wadanda yake zargin cewa suna samun makamai daga kasar Iran.

Mufti Abul Aziz ya fito daga tsatson Sheikh Mohammed bin Abdul Wahhab wanda ya kafa akidojin Wahabiyya a karni na 18 a Saudiyya.

A ‘yan kwanakin da suka shude Jaridar daily newspaper ta Makkah ta rawaito cewa Shehin ya ce ‘yan Shi’ ba Musulmai bane,abinda ya haifar da fushin shugannin addinin kasar Iran.

Kusan maniyyata milyan 1 da rabi wadanda suka fito da sassa daban na duniya ne suka fara aikin hajji a ranar Asabar 10 ga watan Satumbar shekarar bana

You may also like