Shugaban kungiyar Izalar Naijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya zama Shugaban Ahlus Sunnah na Uorope baki-daya, bayan karba gayyatar kungiyar Sautus Sunnah Uorope ta kasar Turai.
Haka Zalika kungiyar Sautus Sunnah Urope ta gina wa kungiyar Izala Ofishi, a cibiyar Ahlus Sunnah ta Turai baki-daya.
“Mun yi nazarin kungiyoyi-kungiyoyi na Musulunci da Ahlus Sunnah a duniya, sama da kungiyoyi sittin (60), a kasashe daban-daban. Amma ba mu ga kungiyar da Allah Ya ba nasara cikin takaitaccen lokaci irin wadda Ya ba kungiyar Izala ba”, Inji Jagororin Kungiyar Sautus Sunnah Uorope ta kasar Turai.