Sheikh Nyass Ya Bada Gudunmawa Wajen Ci Gaban Addini A Duniya – Buhari


Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa Sheikh Ibrahim Inyass ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban addinin Musulunci a nahiyoyin Afrika, Asiya da Turai ta hanyar rubuce rubucensa.

Buhari ya yi wannan ikirarin ne a wurin bikin Maulidin da aka yi a Abuja wanda Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya wakilce shi inda ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da hadin kai ga mabiya Darikar Tijjaniyya don wanzuwar zaman lafiya a kasa sannan ya nemi a ci gaba da yi wa Nijeriya Addu’o’i.

A nasa bangaren, Fitaccen malamin addinan nan, Sheik Dahiru Usman Bauchi ya kalubalanci ‘yan Darikar Tijjaniyyar kan su tabbatar sun mallaki karin zabe inda ya bayyana shi a matsayin Babban makami da za a yi amfani da shi wajen zaben shugabanni nagari.

Haka nan kuma Sheik Dahiru ya yi karin haske kan makasudin yin Mauludin Sheik Ibrahim Inyass inda ya bayyana cewa malamin ya bar abin koyi a duniyar Musulunci. Ya kara da cewa mabiya Darikar Tjjaniya sun yi amfani da bikin Mauludin wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya.

You may also like