Shekarar 2017 Zata Kasance Abin Farin Ciki Gay ‘Yan Nijeriya- Shugaba Buhari


Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shekara ta 2017, mai kamawa za ta kasance shekarar da ‘yan Nijeriya za su dara tare da samun farin ciki da annashuwa. 

“Ina sanar da duk wani dan Nijeriya cewa, nan da farkon shekara mai kamawa ta 2017 akwai babban albishir da zai zo a kasar nan wanda kowa da kowa zai fita daga kuncin rashin ababan more rayuwa. 
“A baya ‘yan Nijeriya sun sha jin irin wadannan kalamai daga bakunan wasu daga cikin jami’an gwamnati na. amma ina tabbatar muku da cewa wannan alwashi dab yake da tabbata da yardar Allah, Inji Shugaba Buhari


Like it? Share with your friends!

0

You may also like