Shekarau Ne Zabin Mu A 2019 –  Matasan ArewaGamayyar Kungiyar Matasan Arewacin Nijeriya sun fito fili inda suka bayyana goyan bayansu ga tsohon Gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau, a matsayin mutum guda daya tilo da ya saura a yankin arewa wanda zai iya jagorantar mulkin kasar nan har ya kai kasar ga tudun mun tsira. 
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa wacce ta samu sanya hannun Shugaban Kungiyar na kasa baki daya Alhaji Imrana Nas kuma aka rarraraba ta ga manema labarai a Kaduna. 
Matasan sun bayyana cewar bayan dogon nazari da bincike da suka gudanar akan manyan Arewa, a karshen al’amari Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau kadai suka gano a matsayin wanda zai iya jan ragamar mulkin kasar nan a shekarar zabe ta 2019 dake tafe. 
Matasan arewan sun bukaci jama’ar Arewa da sauran jama’ar Nijeriya baki daya da su marawa Tsohon Gwamnan na jihar Kano Shekarau baya a zaben dake tafe, domin fitar da kasar daga cikin halin kuncin da take ciki.

You may also like