Shekarau Ya Yi Kira Ga Ƴan Siyasa Da su Fito Su Taimakawa Al’umma


Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan ilimi wanda yake neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Malam Ibrahim Shekarau ya yi kira da kanana da manyan ‘yan siyasa da su fito su taimakawa al’umma a yanayin da ake ciki, ba wai sa lokacin zabe ba su fito suna siyan kuri’a.

Malam Shekarau ya yi wannan jawabin ne yayin ganawar sa da dan takarar majalisar tarayya na karamar hukumar Nassarawa Ambassada Auwal Alhassan Gama, inda ya yaba masa bisa tallafawa matasa da maray da masu karamin karfi da yake yi a karamar hukumar Nassarawa.

Sannan ya jawo hankulan ‘yan siyasa akan su yi koyi da Ambassada Auwal Alhassan Gama wajen tallafawa marasa galihu da marayu saboda motsi ya fi labewa.

You may also like