Yau 3 ga watan Agusta al’ummar Jamhuriyar Nijar ke bukin cika shekaru 56 da samun ‘yancin kai daga Turawan Faransa da suka yi wa kasar mulkin mallaka.
Nijar ta samu ‘Yancin kai ne a 1960.
Shugaban kasa Mahammadu Issoufou, ya yi wa ‘yan kasar jawabi, inda ya tabo kokarin da ya ke yi ta fannin tsaro da kiwon lafiya da ilmi.
A cikin jawabin, shugaban ya jajantawa iyalan Sojojin Nijar da suka mutu a yaki da Mayakan Boko Haram.
Shugaba Issoufou ya jaddada burin shi na kawar da yunwa ta hanyar tsarin dan Nijar ya ci da dan Nijar.
Ana amfani da ranar domin shuka itace don magance kwararowar Hamada kuma Sojojin da suka hambarar da gwamnatin Diori Hamani a 1975 suka bukaci shuka itacen.