
A farkon watan Fabrairu shekara ta 2011 ne mulkin Mua’mar Gaddafi ya gamu da barazana sakamakon zanga zangar da ta barke a wasu kasashen Larabawa wacce nan take ta juye zuwa yakin basasa a kasar ta Libiya.
Gaddafi ya rasa ran sa ne a cikin wani yanayi wanda har yanzu ake ta tababa a kai, bayan da ‘yan tawaye CNT dake samun goyan bayan kawacen sojin da kasashen Biritaniya da Faransa ke jagoranta suka karbe garin Tripoli cikin watan Agusta na shekara ta 2011.
Bayan hakan ne Gaddafi ya koma Sirte kafin daga bisani su cimma shi, su kashe shi a rana irin ta yau 20 ga watan Octoba na shekara ta 2011.
An dai gano Kanar Gaddafi ne a boye a wata magudanar ruwa ga alama yana yunkurin tserewa daga Sirte a wani ayarin motoci wanda jiragen saman NATO suka kaiwa hari.
Yau dai shekaru biyar kenan da kisan Muammar Gaddafi, saidai kasashen dake ikirarin kawo karshen mulkin danniya a Libiya musamman kan ‘yan tawayen Benghazi, babu wani abun da azo a gani da wannan matakin ya haifar, hasali ma kara samar da matsaloli da dagule al’amura musamman a yankin Sahel.
A watan Maris na shekara 2011 shugabannin kasashen yamma a sahun gaba Shugaba na lokacin Nicolas Sarkozy, suka yi nasara shawo kan kwamitin tsaro na MDD ta hanyar gabatar masa da wani kudiri na samar masu da sansanin soji domin daukan dukkan matakan da suka dace don kare fararen hula.
A bisa wannan dubara ce suka samu damar sanya kafa a Libiya domin kawar da shugaban wanda suka ce ya haukace, a lokacin ne kuma kasashen yammacin da kuma na Larabawa bisa matakin da kasar Rasha ta kauracewa suka samu damar kai farmaki a kasar ta Libiya wanda suka ce na hana zubar da jini ne a Benghazi inda nan ne tushen boren daya kawo karshen mulkin shekaru 42 na Kanal Gaddafi.
To aman masana na ganin cewa idan har shigar kasashen yamma da ‘yan amshen shatansu irinsu Saudiyya ya kai ga kifar da gwamnatin wacen lokacin da kuma kashe Gaddafin, to mi akayi kenan a yanzu da kasar ta shiga cikin rudani ta kuma fada cikin hannun gungun mayaka sai kuma uwa uba ‘yan ta’adda irinsu (IS) da sukayi kaka-gida a wasu sassan kasar, ga gwamnatoci biyu masu gaba da juna dake shugabancin kasar, baya ga mumunan koma baya da tattalin arzikin kasar yake fama dashi.
Ga manya manya makaman yaki da mayaka da suka bazu tsakanin kasashe makofata irinsu Nijar, Mali, da Tunisiya.
.Dayewa daga cikin masu sharhi kan lamuran yau da kulun na ganin kasashen yamma basu tunanin yadda zata kasance bayan kifar da Shugaba Gaddafin, don ko ba komi a lokacin gwamnatinsa ta taka mahimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro da kuma yaki da kwararar bakin haure dake rasa sahara zuwa Turai wanda yanzu haka ya kasance babban kalubale ga kasashen Turan.
Wani tsohon jami’in majalisar CNT wace ta kasance kungiyar ‘yan tawaye a lokacin mulkin Gaddafi, kafin daga bisani kasahen yamma su amunce da ita a matsayin majalisar shawara ta wucin gadi a Libiya, Mahmoud Jibril ya bayyana cewa kasahen yamma basu tunani na samar da wani shiri bayan kifar da Gaddafi ba.
Hasali ma da mun tuntube su sai su ce ”su sun gama nasu aiki”
Wannan dai shi yake kara tabbatar da cewa babu wani ci gaba ko gyara da kasancewar sojijin kasashen yamma zai iya haifarwa a wata kasa illah kara dagule al’amuranta.