Shekau Na Farko Da Shekau Na Biyu Sun Mutu-Sojin Nijeriya


 

 

A jiya Alhamis ne Kwamandan rundunar sojin nan ta “Operation Lafiya Dole” da ke yaki da kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram Manjo janar Lucky Irabor ya tabbatar da cewar shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da ma duk wani wanda kungiyar ta taba sakawa a madadin Shekau din sun mutu.

Janar Irabor ya fadi hakan ne a yayin da ya ke zantawa da manema labarai a lokacin da rundunar tasa za ta shiga jahar Adamawa a wani bangare na gabatar da aikinta “Zan iya tabbatar muku da cewa mun kashe Shekau na ainahi, a inda kwanaki kadan da suka gabata a harin da muka kai wa ‘yan ta’addan ta sama muka raunata wanda ke basaja a matsayin Shekau. Sai dai ba mu da tabbaci zuwa yanzu ko ya mutu ko bai mutu ba”.

 

Janar Irabor ya ci gaba da cewa, “Sun saki wannan bidiyon ne don su nuna cewa har yanzu suna da karfi, amma a hakikanin gaskiya, dodo-rido ne kawai”.

 

Irabor ya kara cewa “Rundunar soji bata fid da wani rahoto wanda ya ke ba na gaskiya ba”

 

Kwamandan ya tabbatar da cewa rudanar sojin Nijeriya da ke yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashi kasar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta tabbatar da kakkabe ta’addanci da ‘yan ta’adda a yakin.

You may also like