Shekau Ya Fitar Da Sabon Bidiyo, Inda Ya Musalta Cewa Ya Samu Rauni,Ya Kuma Ci Alwashin Cigaba Da Kashe Mutane 


Abubakar Shekau Jagoran kungiyar Boko Haram ya fitar da wani Sabon fefan bidiyo inda a ciki yake musalta cewa ya samu rauni sakamakon harin da sojin Najeriya suka kai musu yayin da suke gabatar da sallar juma’a a makon da ya gabata.

Akwai rahotannin dake nuni da cewa shekau ya samu rauni,yayin da wasu daga cikin magoya bayansa suka rasa ransu lokacin da suka taru don gabatar da sallar juma’a a kusa da Damboa.

Amma a sabon fefan bidiyon da yafitar mai tsawon minti 14 shekau ya zargi jami’an sojin Najeriya da yada karya. 

Ya cika bakin cewa lokacin mutuwar sa baiyi ba tukunna, kuma zai kashe mutane da dama a nan gaba.

“kunyi ikirarin cewa jirgin ku yakai hari a kan taron mu lokacin da muke gabatar da sallar juma’a,kuka kashe wasu daga cikin mu, ni kuma na samu rauni, a kusa da Damboa ni ban taba jin sunan garin ba.

“Tun farko kunce Ina Sambisa , yanzu kuma kunce Ina kusa da Damboa, baza ku taba sanin inda nake ba, Allah yakare ni daga ganinku Saboda inayin abinda yakeso ,kuyi kara hakuri idan lokaci na yazo karshe a duniya , zan mutu babu abinda zai same ni. 

” Bamu damu ba, muna wannan bidiyon ne Saboda mu karyata farfaganda da ake yadawa, mutane masu yaudara karshensu na karewa da kunya,Shekau yana nan da ransa, banfara kisa da sunan addini ba, amma zan fara a nan gaba “


Like it? Share with your friends!

0

You may also like