Shugaban kungiyar boko haram Abubakar Shekau ya bayyana a wani sabon bidiyo, da aka fitar a yau Jumu’a inda ya musalta ikirarin da shugaban kasar Kamaru Paul Biya yayi na kaiwa kungiyar hari, shugaban yakuma yi barazana ga shugabanni duniya.
Bidiyon mai tsawon minti 27 wanda jaridar PREMIUM TIMES ta samu ta hannun wani dan jarida me alaka da kungiyar ya nuna shekau na godewa magoya bayansa.
Har ila yau shekau yanuna wasu katin shaida, harsashi da wasu kayayyaki dake nuni da cewa an kwace su daga sojojin kamarun.
Shekau ya umarci mabiyansa da suka sance cikin shiri da biyayya inda yace kungiyar baza ta gajiya ba har sai an tabbatar da shari’a a kasashen:Benin, Najeriya, Kamaru,Chadji da Nijer.