Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fito da sabon faifan bidiyo inda ya nuna wasu ‘yan Matan Chibok su kusan 14 wadanda suka yi ikirarin cewa ba za su rabu da kungiyar ba kasancewa Shekau ya rigaya ya aurar da su ga wasu ‘ya’yan kungiyar.
Haka ma, a cikin bidiyon na mintoci 20, ya nuna wani jirgin yakin sojojin Nijeriya wanda ya ce mayakansa ne suka harbo shi. Haka nan, ya nuna sauran kayayyakin yaki na sojojin Nijeriya da suka kwace har da wani jirgi sama mara matuki.