Shekau Yace Yanzu aka Fara Kai Hare-Hare A Wani Sabon Fefan Bidiyo Da Yafitar Kan Harin Birnin Maiduguri Na Ranar Laraba Jagoran kungiyar Boko Haram  Abubakar Shekau yafitar da wani Sabon fefan bidiyo wanda yanuna yadda yan ta’adda suka kori sojoji da Ke wani wuri a wajen birnin Maiduguri. 

Yan ta’addar sun kori sojojin kafin su karasa sukai hari kan al’ummar jiddari. 

Bidiyon na tsawon minti 33 yanuna Shekau yana rike da kakin sojoji,  harsashi da sauran kayayyakin da suka samu daga wurin sojojin da suka gudu. 

” Yanzu aka fara ,” shekau yana cewa a cikin bidiyon. 

Ya karyata cewa suna dajin Sambisa inda yace suna nan cikin wani yanki na Maiduguri.

Ya kuma ce babu wata tattaunawa tsakaninsu da gwamnati  a kokarin da ake na kawo karshen rikicin. 

You may also like