
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin haƙar ɗanyen man fetur na Shell zai biya diyyar dala miliyan 16 ga wasu manoma a yankin Neja-Delta a kudancin Najeriya.
Hakan na cikin diyyar da kamfani zai biya ga waɗanda malalar man fetur ta yi musu barna a gonakinsu.
Alƙawarin biyan diyyar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a tare da haɗin gwiwar reshen cibiyar Friends of the Earth a ƙasar Netherlands.
Matakin ya biyo bayan hukuncin kotun Netherlands inda ta kama reshen kamfanin na Shell a Najeriya da laifin malalar mai a shekarar da ta wuce kuma ta umarci Shell ya biya diyya.
Tun a shekarar 2008 ne manoma daga Neja-Delta tare da taimakon kungiyar kare hakkin bil adama ta Friends of the Earth suka gurfanar da Shell a gaban kotun da ke The Hague sakamakon gurɓata musu muhalli da ya yi a tsawon shekarun da ya shafe yana haƙo albarkatun fetur a yankin.
Kamfanin Shell ya yi barnar a shekarun 2004 zuwa 2007.
Eric Dooh wanda mahaifinsa na daga cikin manoma da aka yi ta’adi ya ce za a biya diyyar ga kauyukan Oruma da Goi da Ikot Ada Udo.
Malalar mai na ci gaba da barna a yankin Neja Delta lamarin da ke shafar lafiya da kuma rayuwar al’ummar.
Manoma hudun da suka shigar da karar tun farko su ne Barizaa Dooh, Elder Friday Alfred Akpan, Cif Fidelis A Oguru da kuma Alali Efanga.
Kuma a cewarsu malalar ta hanasu noma gonakinsu.