Shiga Jami’a ya haramta ga ‘yan matan da suka rasa budurcinsu


 

 

Kafafen yada labarai na duniya na ci gaba da yiwa wani dan majalisar kasar Masar mai suna Agina dariya sabili da ya ce ya kamata kowace ‘ya mace ta yi gwajin budurci gabanin ta samu izin fara karatu a jami’a.

jaridar Youm 7 ce ta rawaito wannan zancen.

Tuni dai al’umar ciki da wajen kasar ke ci gaba da kiran dan majalisar ta wayar tarho domin rufe shi da hadarin bakaken kalamai.

Karo na farko kenan dan majalisar ta furta irin wannan kalamin wanda ya bakanta wa ‘yan kasar Masar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like