Sojojin Turkiyya sun shiga rana ta 34 fara jagorntar kai hare-haren “Tsaron Firat” a arewacin Siriya wanda aka fara a ranar 24 ga watan Agustan da ya gabata.
Ana ci gaba da samun arangama tsakanin ‘yan ta’addar Daesh da mayakan Free Syrian Army a yankunan Tall Ar, Tall Ashah da Al-Ayyubiyah.
Dakarun Turkiyya kuma sun kai wa ‘yan ta’addar Daesh hari sau 27 a wurare 18.
Majiyoyin soji sun tabbatar da cewa, ya zuwa yanzu an kai hari kan ‘yan ta’adda a arewacin Siriya sau dubu 5,034 a wuraren dubu 1,307.
Haka zalika, dakarun kasashen duniya karkashin jagorancin Amurka sun kai hari ta sama kan Daesh tare da kashe ‘yan ta’adda 4.
An kuma lalata wasu manyan bama-bamai da aka binne a kasa.
Tun bayan fara kai hare-haren na Firat an lalata manyan bama-bamai 28 da kuma kanana guda 981.
Hukumomin bayar da agaji na AFAD da Kizilay na ci gaba da bayar da taimako ga wadanda aka jikkata a rikicin.