Shin akwai bukatar gwanati ta tantance malami kafin ya fara wa’azi?



BBC

Masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya na ci gaba da taƙaddama kan kalaman wani malami addinin Musulunci da ake zargi da munana kalamai a kan Annabi Muhammadu.

Mutane da yawa sun yi zargin cewa kalaman Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi game da matsayin Annabi Muhammadu sun yi kaushi kuma ba su dace ba.

Cikin masu mayar da martani har da malaman addinin Musulunci daga ɓangarori daban-daban.

Lamarin har ya kai ga muhawara a kan ko ya kamata gwamnati ta riƙa tantance malaman da ke wa’azi a faɗin ƙasar ko a’a.



Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like