Latsa lasifikar da ke sama don kallon cikkaken bidiyon
A Najeriya tun bayan da babban bankin ƙasar ya fitar da sabbin takardun kuɗin kasar da ya sauya wa fasali, waɗanda suka hada da 200, da 500 da kuma 1000 a ranar 15 ga watan Disambar shekarar da ta gabata, wasu mutane suka fara yaɗa wani ikirari a shafukan sada zumunta.
Ikirarin shi ne cewa idan aka goga musu auduga akan ga kalarsu a jikin audugar, ko idan aka wanke da ruwa sukan koma farar takarda sal!
Shin wannan iƙirarin haka yake? ko kuwa shaci faɗi ne kawai? BBC Hausa ta gwada duka waɗannan ikirari guda biyu da aka yi, ta kuma tabbatar da cewa sam ba haka batun yake ba.
Domin kuwa BBC ta wanke duka sabbin takardun kuɗin tare da tsoffin, har ma da wasu kuɗaɗen ƙasashen waje, domin tabbatarwa.
Abin da kuma BBC ta gano shi ne sam ba haka lamarin yake ba.
Domin kuwa bayan da ta wanke duka takardun kuɗin babu wadda a ciki ta koma farar takarda kamar yadda wasu suka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta.