shin daliban jihar kano zasu samu shiga jami’a


A Nigeria daliban Kano da suka kammala sakandaren gwamnati na fuskantar barazanar rashin samun damar shiga jami’a bana, bayan da gwamnatin jihar ta gaza biyan kudin jarrabawarsu ga hukumar WAEC.
Wannan ya sa hukumar ta WAEC rike sakamakon daliban, batun da ke janyo cece-kuce a jihar tare da jefa daliban cikin rudani.

Lamarin dai ya sa da dama ba su je jarrabawar tantancewa ba a jami’ar da suka nema, yayin da wasu kuma suka yi amfani da sakamako na jira, da fatan samun dacewa.

Wasu daliban da suka tattauna da ‘yan jaridu sun ce sun fidda rai da karatun jami’a a bana, sabo da har lokacin da jami’ar da suka nema ta tantance masu nemar daukarsu karatu, ba su samu sakamakonsu ba, dan haka basu halarci tantancewar ba.

“Gaskiya ban je tantancewa ba, ba sakamako a hannuna wace tantancewa zan je?” a cewar wata daliba.

“Da a ce ma an sa lokacin da zai fito ne shi ne da sauki sai kaje, watakila idan ya fito a yi maka alfarma. Idan da Allah zai sa a taimaka a sakar mana da wuri, sai mu sauya makaranta, ko da makarantrun fasaha ne,” in ji Halima Abba.

Ta kara da cewa A yanzu na fitar da rai da karatun digiri a jami’a a fannin jinya da na jima ina so in yi, tun da lokaci ya riga ya kure”.

Akasarin daliban jihar Kano dai kan nemi karatu a jami’ar Bayero, wadda tuni ta gama tantance masu bukatar shiga karatu a bana.

Ana dai ganin cewa rashin biyan kudin jarrabawar da gwamnatin Kano ba ta yi ba, shi ne ya janyo hukumar shirya jarrabawar kammala sikandare ta Afirka ta yamma WAEC ta ki fitar da sakamakon daliban Kano.

To sai dai gwamnatin a na ta bangaren na cewa ta kammala shiri don ganin an saki sakamakon daliban a cikin wannan makon.

You may also like