
Asalin hoton, OTHER
A jiya ne aka kammala gasar kofin duniya ta Qatar 2022 da Argentina ta yi nasara kan Faransa a wasan karshe.
Hakan na nufin baya ga kofin duniya da sarkar zinari da aka bai wa yan wasa, Argentina za ta bar Qatar da miliyoyin daloli.
A bana hukumar kwallon kafa ta duniya ta ware kudin da za a ci kyauta, da yawansu ya kai dala miliyan 440.
Kasashe 32 daga fadin duniya da suka wakilci nahiyoyinsu za su bar Qatar da akalla dala miliyan tara kowannensu.
Iya matakinka iya kudinka
Dama FIFA ta fitar da abinda kowace kasa za ta samu gwargwadon matakin da ta kai a gasar.
Idan za mu faro daga kasa, kasashen da suka samu damar zuwa gasar amma suka gaza tsallake matakin rukuni za su koma gida ne da dala miliyan tara kowannensu.
Hakan nufin kasashen Qatar, Ecuador, Wales, Iran, Mexico, Saudi Arabia, Denmark, Tunisia, Canada, Belgium, Germany, Costa Rica, Serbia, Cameroon, Ghana, da kuma Uruguay sun samu dala miliyan tara kowannensu.
Sai kuma kasashen da suka samu kai wa zagayen yan 16, amma gudunsu ya kare daga nan, da suka hada da Amurka, Senegal, Australia, Poland, Sfaniya, Japan, Switzerland, da kuma Koriya ta Kudu, kowannensu ya samu dala miliyan 13.
Kazalila wadanda suka samu kansu a zagayen quarter-finals da suka hada da Brazil, Netherlands, Portugal, da kuma England sun samu dala miliyan 17 kowannensu.
Asalin hoton, OTHER
A fagen neman na uku kuwa, ma’ana gurbin da Maroko da Croatia suka samu kansu bayan kaiwa zagayen kusa da karshe, Croatia ta samu dala miliyan 27, yayin da Maroko ta koma gida da dala miliyan 25 a matsayin na hudu.
Sai kuma zagayen karshe da aka warewa dala miliyan 72.
Kuma Faransa da ta yi rashin nasara ita ce mai dala miliyan 30, yayin da Argentina da ta lashe kofi za ta koma gida da dala miliyan 42.
FIFA ta kara yawan kudin da za a ci idan aka kwatanta da wasannin baya da dala miliyan 40.
Hakan na nufin a 2018 kasashen da suka samu halartar gasar sun raba dala miliyan 400 ne.
Kafin 2006 kasashen da kesuka lashe gasar kofin duniya ba su taba wuce karbar sama da dala miliyan 10 ba.
Italiya ma da ta lashe kofin duniya a 1982 dala miliyan 2.2 kawai ta samu.
A ina FIFA ke samun kudadenta?
Tamabayar cewa a ina hukumar kwallon kafa ke samun kudade tana da saukin amsawa- ta hanyar shirya gasa!
A gasar kofin duniya ta 2018 kawai, FIFA ta samu sama da dala biliyan 4.6 na kudin shiga.
Kuma kusan duk shekara hukumar bata rasa wata gasa da zata shirya, duk da ba lalle ta samu makudan kudade ba kamar a gasar kofin duniya ta maza ba.
A 2021 ne ma da bata shirya gasa ba, amma duk da haka sai da FIFA ta cika asusunta da dala miliyan 766.
Asalin hoton, OTHER
Mafi yawan ribar da FIFA ke samu na fitowa ne ta hanyar kudaden da ake biyanta don samun damar nuna wasannin kofin duniya da sauran gasa daban-daban da take shiryawa.
Gasar kofin duniya ce abunda aka fi kallo a duk duniya, inda aka yi hasashen biliyoyi za su kallo gasar Qatar 2022.
A gasar kofin duniya ta wadda Rasha ta karbi bakunci, sama da mutum biliyan hudu ne suka kalli wasan ta talabijin da sauran kafofi na zamani.
Haka kuma FIFA na karbar makudan kudade ga kamfanoni da ke tallar hajojinsu a lokacin da gasa ke gudana.
Tun kafin fara gasar 2018 FIFA ta ta samu kusan dala biyan biyu daga kamfanonin da ke son FIFA ta yi musu talla a gasar.
Asalin hoton, OTHER
Kazalika wasu kamfanoni kamar na gyam na bidiyo da ya shafi kwallon kafa na biyan FIFA makudan kudade don amfani da sunanta.
Kamfanin gyam din bidiyo na EASPORTS da ke Amurka ya bai wa FIFA dala biliyan 20 don amfani da sunanta a tsawon shekaru 20.
Wata hanyar kuma da FIFA ke samun kudin shiga itace sayar da tikitin shiga kallon wasanni.
Kusan tikiti miliyan uku FIFA ta sayar ga wadanda ke son kallon gasar Qatar 2022 da aka kammala.
Kuma farashin tikitin na farawa ne daga dala 100 zuwa dala 1,100.
Saboda haka ko a tikiti kawai FIFA na samun biliyoyin daloli na kudin shiga.