An fara hasashen cewa Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu zai bar hukumar bisa karin girman da aka yi masa kwanan nan inda ya zama cikakken Kwamishinan ‘yan sanda.
A bisa ka’idar aiki, dole Magu ya tafi kwas a cibiyar horas da manyan jami’an gwamnati da ke Kuru a jihar Filato a matsayinsa na Kwamishinan ‘yan sanda. Wasu na ganin wannan zai inganta dangantaka tsakanin bangaren gwamnati da na majalisa idan har Magu ya koma Makaranta.