Shin me ya sa hare-haren ‘yan fashin daji ke dawowa a Najeriya?bandits

Asalin hoton, Getty Images

Ana ci gaba da nuna fargaba a Najeriya saboda ƙaruwar hare-haren ‘yan fashin daji a sassan arewacin ƙasar, kwanaki ƙalilan bayan kammala zaɓuka.

A ranar Lahadi ne, gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da kashe gomman mutane da raba ɗumbin wasu da mutsugunansu a ƙauyen Aloko cikin yankin Dekina, bayan wani harin wasu ‘yan bindiga da ba a tantanace ko su wane ne ba.

Gwamnati ta ce maharan waɗanda yawansu ya kai kusan 100 sun kai hari yankin ne, daga sansaninsu da ke maƙwabtaka.

Harin na zuwa ne daidai lokacin da wasu ‘yan bindiga suka sace ɗalibai kusan guda 10 a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna. An kuma samu irin wannan hari da ya yi sanadin sace ɗalibai mata biyu daga Jami’ar Tarayya ta Gusau a jihar Zamfara mai maƙwabtaka.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like