Shin MOPPAN ta yi wa Rahama Sadau aldalci ?


 

Shin MOPPAN ta yi wa Rahama Sadau aldalci ?

Tambayar kenan da dubban mutane ke ci gaba yi dangane shawarar korar Rahama Sadau daga masana’antar Kannywood da kungiyar mashiryan fina-finai ta arewacin Najeriya ta yanke.

Ganin irin yadda mashahuruen ‘yan wasa kamar su Ali Nuhu da Sani Musa Danja ke ci gaba da shagalinsu a fina-finan kudu ba tare da wata doka ta taba hau kansu ba.

A ‘yan kwanakin da suka shige, MOPPAN ta yi wa shahararriyar ‘yar wasan Hausa Rahama Sadau korar har abada daga masana’antar Kannywood sakamakon rungumar wani mawaki mai suna Classic da ta yi a cikin wani faifan bidiyo.

A lokacin da yake furta albarkacin bakinsa,shugaban MOPPAN Salisu Mohamed ya ce “Tauraron ‘yar wasa Rahama ya dushe,domin ba zata kara fito a fina-finan Hausa ba,sakamakon irin gurbataccen halin da ta nuna wa duniya”.

A Najeriya dai dabi’un al’umomin kudancin kasar sun sha bamban da na jihohin 12 da ke a arewaci,wadanda suka kafa shari’ar Musulunci tun a shekarar 1999 tare hana kafuwar masana’antar fina-finai ga baki daya.

Amma da yake dubban mutane ne ke cin moriyar wannan masana’antar wacce ita ce ta 2 a duniya, sai hakar malaman arewancin kasar ya kasa cimma ruwa.

Bayan sun kwashi wani zamani suna cece-kuce kan wannan batun,sai mu’addiban da kuma masu ruwa da tsaki a harkar fina-finan Hausa suka cimma matsaya, inda a gindiya musu sharudan gudanar da sana’arsu ba tare da sun taka dokokin shari’ar Musulunci ba.

A cikin wani sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter,Rahama Sadau ta nemi gafara a gun masoyanta da kuma daukacin al’umar Aerwa.Amma ga dukkanin alamu, da wuya MOPPAN ta lashe amman da ta yi.

You may also like