Shin Ya Kamata A Daina Sa Bayanin Addini Da Asalin Inda Mutum Ya Fito A CV
A daidai lokacin da ake neman hanyoyin samar wa matasa masu zaman kashe wando ayyukan yi da kuma warware rikice-rikice masu nasaba da kabilanci da banbance-banbancen addini da wasu lokutan a ke nunawa a fannin daukan aiki a Najeriya, wasu matasa da masana kundin tsarin mulki na ganin cewa ya dace a cire bayanin addinni da asalin jihar da mutum ya fito a takardar bayanin mai neman aiki wato CV don rage matsalolin kabilanci a kasar.

ABUJA, NIGERIA – Matasa ‘yan Najeriyan dai sun fara yin kiraye-kirayen a daina sa bayanin asalin jihar da mutum ya fito da kuma addininsa a takardar bayanin mai neman aiki wato CV ne a kafaffen sada zumunta inda su ke cewa hakan zai taimaka wajen ba wa wadanda suka kware aiki ba tare da la’akari addininsu da inda suka fito ba, baya ga rage matsalolin da suka shafi kabilanci da nuna banbancin addinin wajen daukan aiki.

Ko menene kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar a game da wannan batun, fitaccen lauya barrister Mainasara Kogo ya ce maganar CV ya na da amfani idan za abi adalci da gaskiya a cikin kasa, wato ma’ana idan za abi wani tsarin mulkin kundin kasa da ya ce ayi daidaito wajen duba halaye masu kyau, amma idan hakan zai kawo rashin bin adalci to za a saba ga wani fannen tsarin mulkin kundin kasar.

Tun ba yau ba ake fama da matsalolin da suka shafi rashin yin daidaito wajen daukan aiki a ma’akatun gwamnati da ma kamfanoni masu zaman kansu kuma a wasu lokutan ake danganta kin daukan mutum aiki ga kiyayya ga asalin shiyyar da ya fito ko banbancin addini da dai sauransu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:

You may also like