Shinkafar Roba Na Janyo Toshewar Hanji – Dakta Salihu KwaifiA yayin da ake ci gaba da korafe korafe kan yadda wasu ‘yan kasuwa ke shigowa da shinkafar da ake yi da roba daga China, wani ƙwararren likita a asibitin Wuse da ke Abuja Dr. Salihu Ibrahim Kwaifa ya ce shinkafar robar zata iya haddasa toshewar hanjin mutum lamarin da ka iya kaiwa ga yin tiyatar gaggawa.
Tun da farko dai, Masana a harkar kiwon lafiya  sun ce idan har ta tabbata cewa shinkafar da hukumar hana fasa ƙwauri ta kasar ta kama da roba a cikinta, to za ta iya lahani ga bil’adama musamman cutar Kansa (Cancer).
Hukumar ta kwastam dai ta bayyana cewa ta kama buhu sama da dari na shinkafar roba da aka shigar da ita ƙasar ta harmtacciyar hanya. Wani babban jami’in hukumar ya ce wani dan kasuwa ne ya shigar da shinkafar domin sayarwa a lokacin bukuwan kirsimeti.

You may also like