An Shira Wa Alkalai Taron Bita A Kebbi


 

 

Babbar kotun daukaka kara ta Shari’ar musulunci ta jihar Kebbi  ta shirya wani taron horarwa na kwana uku ga Alkallanta da Jami’ai masu sa ido akan ayyunkan kotutukan  Shari’ar musulunci na  jihar domin kara inganta  ayyukan kotutukan, musamman  ta fanin i’imin Shari’a na kasar nan, da kuma gano abubuwan da suke damun kotunan  ta fuskar Shari’a da makamantansu.

A cikin jawabinsa wajen bude wannan taro, babban Alkalin Alkalan jihar Kebbi, Khadi Muktar Imam Jega ya bayyana cewa sun shirya wannan taro ne domin ilimantar da Alkalan, musamman hanyoyin da za su inganta aikinsu, wanda kuma aka shirya wa Alkallan  da ke karkasa. Taron yan gudana ne Birnin-kebbi a makon da ya gabata.

Ya ci gaba da cewa an zabo mahalartan taron ne daga  kotututa Shari’ar musulunci ta jihar Kebbi, wacce kuma za ta dauki  kwana uku. Daga nan ya yi kira ga mahalarta taron a kan su tsaya su koyi abin da su ka zo yi, domin ta haka ne  Hukumar gidan Shari’a za su iya magance matsalolin kotutunan.

Shugaban ya ja hankali Alkallan da su dinga yada ayyukan kotutukan Shari’a a kafafen watsa labarai domin zama shaida, ko abin misali ga al’umma, kuma ya zama matsayin ci gaban ilimin masu Shari’a a kasar nan. Inda kuma ya ja kunen Alkallan da su gudanar da ayyuka su yadda yada ce.

Da yake jawabinsa tun farko, Gwamna jihar kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana godiyarsa ga Alkalin Alkalan game da irin wannan muhimmin tunani da ya yi na horar da Alkalan.

Gwamna, wanda Mataimakinsa, Samaila Yombe Dabai ya wakita, ya kuma bukaci mahalar taron su yi amfani da abin da suka koya domin ciyar da kotutukan Shari’ar musulunci gaba. Kana kuma  ya nuna gamsuwarsa da goyon bayan gwamnatinsa ga wannan shiri.

Wannan taro dai ya samu halartar mayan Shugabannin gwamnati, kamar Kwamishiniyar Shari’a ta jihar, Hajiya Rakiya Tanko Ayuba, Babban Alkali na jihar Kebbi, Hon. Bala Mairiga, Babban  Magatakardar kotun daukaka karar Shari’a musulunci, Alhaji Muhammad Sani Randali da sauran bakin da aka gagyato.

You may also like