SHIRIN AUREN ZAWARAWA A KANO: Zawarawa Da ‘Yan Mata 10,000 Sun Yi Rijista


 

Shirin auren zaurawa da gwamnatin Kano ke shiryawa,  Hukumar Hizba ta jihar ta ce sama da zaurawa da ‘yan mata fiye da dubu goma ne suka yi rajista domin su amfana daga tsarin na auren Zaurawa da ‘yan mata.

Masu shirya auren sun ce matakin na taimakawa wajen rage adadin zaurawa da ‘yan mata da ke neman mazan aure a jihar.

Sai dai ba wannan ne karon farko da gwamnatin jihar Kano ke aurar da zawarawa da ‘yan mata ba a jihar, kuma masu kudi da ‘yan kasuwa na kawo ta su gudummawar don cigaban shirin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like