Shirin Buhari na daukar matasa aiki a Najeriya


 

 

Matasan da za su yi aiki a makarantu da gonaki da ma asibitoci na kasar dai na zaman wani yunkuri na inganta muhimman harkokin da kasar ke fata za su taimaka a kokari na kaita tudun mun tsira.

Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari (picture-alliance/AP Photo/S. Alamba)

Bayan share tsawon wata da watanni ana jiran tsammani gwamnatin Najeriya a ranar Litinin din nan (21.11.2016) ta fitar da sunayen wasu jeri na matasa dubu 200 da ta ce za ta yi aiki da su na tsawon wasu shekaru biyu da niyyar habbaka harkokin noma da ilimi da lafiya.

Jerin na matasan da suka fito daga sassa daban daban na Najeriyar dai na zaman matakin farko a hanyar cika alakawari na gwamnatin kasar na daukar dubu 500 aiki.

Nigeria Makoko schwimmende Schule in Lagos (Reuters/A. Akinleye)

Kowane a cikin matasan 200,000 dai zai samu horo na musamman sannan kuma da naurar kwamputa da zai rika amfani da ita har na tsawon shekaru biyun da ke tafe.

Laolu Akande dai na zaman kakaki na mataimakin shugaban kasar kuma jagoran shirin da ke da taken Npower.

“Ba kawai za su yi aiki  a matsayin malaman makaranta ko kuma na lafiya ko kuma turawan gona ba, za kuma a ba su horaswa ta inganta rayuwa ta yadda a karshen shekaru biyu za su dauki aikin din-din-din ko kuma su samu damar iya rikidewa zuwa mamallaka na sana’oi.”

Nneota Egbe (Channels TV)

A fadar Abdul Azeez Yari Abubakar da ke zaman gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban gwamnoni na kasar suma ragowar  jihohin da su ka gaza hobbassan za su samu kari na masu shiga cikin shirin da zai zamo damar daukar aiki mafi girma ga sabuwa ta gwamnatin.

Ko bayan kashi na farkon da zasu fara aiki ranar daya ga watan gobe na Disamba, gwamnatin na kuma fatan sake daukar wasu karin 300,000 da nufin kaiwa ga burinta na aiki ga matasa Dubu 500  cikin kasar.

You may also like