- Marubuci, Daga Jean Mackenzie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai aiko da rahotanni daga Seoul

Mata a Seoul na zanga-zanga kan shirin gwamnati na rusa daidaiton jinsi a ma’aikatu
A rana ta farko da Yuna ta fara zuwa aiki, a matsayin akanta a wani banki, ba ta taɓa zaton za ta gamu da wani aikin na daban saɓanin wanda aka ɗauke ta a kansa ba. Wato dafawa abokan aikinta abincin rana.
Daga bisani, an buƙaci ta je ta wanke duk ƙyallayen goge hannu da abokan aikinta maza suka yi amfani da su.
An ce aikinta ne, kuma dole ta yi. Da farko ta ɗauka wasa ne, ta kuma ce ba za ta wanke ba.
Da ta tambaye su ko me ya sa ba za su iya ɗauke ƙyallayen da suka yi goge-goge su wanke a gida ba?
Ga mamakinta, sai shugaban wurin ya ka da baki ya ce; ”Ta yaya za ki ce maza su yi wankin tsummokara?”
Cikin fushi da ɓacin rai ya yi maganar ta kuma lura idan ta ƙara cewa uffan, cin mutuncin zai wuce haka, sai kawai ta ɗauka ta fara wankewa.
Ƙorafin da ta yi ya sa ta shiga baƙin littafin shugaban wurin aikin.
Lokacin da take tafiya a wata kasuwa da ke kusa da inda take zaune, sanye da tufafi launin fari da baƙi na ‘yan wasan ƙwallon kwando, da hula hana sallah, da wando buje, da riga bunjimemiya don ɓad da kama.
Wannan wani ɗan ƙaramin gari ne, ta kuma yi wani abu da ya kamata a kore ta daga aiki.
Saboda ta ɗauki bidiyon duk abin da ya faru a wurin aiki tare da maka ƙorafin bankin ga hukuma, don gudanar da bincike..
Yuna ta ɗauki bidiyon lokacin da take dafa abinci don abokan aikinta, ta kuma yi amfani da shi wajen kai ƙorafi ga gwamnati
Koriya ta Kudu ta yi fice wajen raya al’adu da fasahar zamani, sai dai a ƙoƙarin da take na kawo sauyi da zama ɗaya daga cikin ƙasashe masu taƙama da arziƙi a duniya, an tafi an bar mata a baya.
Albashin ma’aikata mata da maza ya sha bamban, ana kuma bai wa maza fifiko ta kowacce fuska.
Kashi 5.8 ne kaɗai na matan Koriya ta Kudu suke aikin ofis, yayin da sauran ke zaman gida da kula da iyali ko kasuwancin da bai taka kara ya karya ba.
Su ne kula da iyali da rainon yara da kula da iyaye tsofaffi, da ‘yan makaranta da girki da sauransu.
Duk kiraye-kirayen da ake yi na tabbatar da daidaito, amma shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol, ya kafe cewa duk abubuwan da ake faɗa ba gaskiya ba ne an daɗe da ganin shuɗewarsu.
Shi kansa shugaban ƙasar da ƙyar ya naɗa mata uku a majalisar ministocinsa mai kujera 19.
A yanzu ma yana ƙoƙarin rusa ma’aikatar tabbatar da daidaito wadda yake ganin ta bai wa mata ‘yanci da tallafin ɗaga muryarsu da neman ‘yanci.
Masu zanga-zanga sama da dubu 800 ne suka taru don hana rufe ma’aikatar.
Yawancin matasan Koriya sun ce ana yawan takura musu
Daga cikin masu fatan kawo sauyi da kawar da hakan akwai Park Ji-hyun, ‘yar shekara 28, da ke gangamin kwatarwa mata ‘yanci a wuraren aiki, sannan an buƙaci ta zama jagorar jam’iyyar ‘yan adawa ta masu ra’ayin sassauci.
Duk da yake ba ta taɓa shiga siyasa ba, amma ta amince da wannan tayin.
A lokacin da muka haɗu a kantin sayar da Gahawa da ke wajen birnin Seoul, ta shaida min muƙamin ya kuɓuce mata.
Dole ta sanya ta guduwa daga gida saboda an yaɗa adireshinta a intanet, bayan fara turo mata saƙonnin barazanar ɓata mata fuska da ruwan asid.
Ta ce watanni shida ne masu tsauri a rayuwarta, ta shaida min barazanar cin zarafi, da ta yi mata fyaɗe, sun sanya dole ta fara wasan ɓuya.
Ta kasance ita kaɗai ce mace a tsakanin abokan aikinta, kuma ko ana taro idan ta yi magana sai duk su yi biris da ita.
”Lokacin da nake son tattaunawa kan tattalin arziƙi da muhalli, abin da suke faɗa min shi ne ke mace ce, ki mayar da hankali a kan abin da ya shafe ki, me mece ta sani a wannan fannin?” wannan shi ne halin da na shiga.
Ta yi fama da tsangwama lokacin da take shugabar mata a jam’iyyar Liberal
Park ta samu ɗaukaka da fice tun tana ɗalibar nazarin aikin jarida, lokacin da ta bankaɗo badaƙalar wata ƙungiya ta intanet da ke tilasta wa mutane aikata jima’i ta hanyar yi musu barazana.
Bayan ta bankaɗo su ne aka tusa ƙeyar shugaban zuwa gidan yari, to amma har yanzu ana fama da wannan matsalar.
Ko a bara an samu ƙorafi 11,568 na laifukan cin zarafi ta hanyar lalata a intanet, adadin da ya ruɓanya wanda aka gani a shekarar da ta wuce.
Lokacin da aka kai su gidan yari, matan da Park ta taimaka a baya, sun shirya mata ƙwarya-ƙwaryar liyafa.
“Lokacin da muke tattaunawa wata mai kawo abinci ta kawo mana kek, a nan ne kuma matan suka kalli Park tare da cewa; ”Muna matuƙar godiya da taimakon da kika yi mana”.
Kunya ce ta rufe Park, ta fara murmushi. Takitaccen lokacin da ta yi aiki da ‘yan siyasa ta zama wata abar kwatance da koyi kan batutuwan haƙƙin mata.
A Koriya ta Kudu an kirkiri maudu’in #MeToo na fafutukar hakkin mata da ya tada kura
A 2018 ne, aka fara gagarumin gangami irinsa na farko a yankin Asiya, gangamin kare ‘yancin mata kuma a nan ne aka ƙirƙiri maudu’in #MeToo movement a shufukan sada zumunta.
Ba da jimawa ba takwarorinsu maza suka fantsama tituna da shafukan sada zumunta suna ɓata wa mata suna, da ƙorafin cewa matan na neman fin ƙarfin kowa a cikin al’umma.
Sun kuma yi ƙorafi kan aikin soji na dole da ake tura su amma ba a tura mata, sun yi nasarar shafa wa masu fafutukar kare ‘yancin mata bakin fenti.
Wata nasara da matan suka yi ita ce samun shugaba da ta ji koken su. “An takura wa mata an hana su ‘yancinsu, amma wannan karon za a ga sauyi,” in ji Lee Jun-seok mai shekara 37, wadda ita ce ta jagoranci, gangamin.
Ta kara da cewa ana buƙatar dokar da za ta kawo didaito tsakanin maza da mata a wuraren aiki, ko makarantu da sauransu.
Shekaru 6 da suka wuce aka yi wa Ana fyade, ta ce ma’aikatar daidaiton jinsi ta taimaka mata ƙwarai
Shekaru shida da suka wuce ne aka yi wa Ana mummunan fyade, kuma ta ce ma’ikatar daidaiton jinsi sun taimaka mata ta hanyoyi da dama.
Sun sama mata wurin zama mai cike da tsaro, sun kuma kai ta asibiti tare da haɗa ta da wanda zai dinga taimaka mata duk damuwarta ta yaye.
”Taimakon da ma’aikatar ta yi min ya ninka wanda ‘yan uwana suka yi min,” in ji Ana.
Farfesan makarantar da Ana ke halarta ne ya yi mata fyaɗe, hukumomi sun yi tsayin daka har sai da suka ƙwato mata ‘yanci, yanzu haka yana zaman gidan yari don hukuncin da aka yanke masa.
Sai dai duk da haka tana yawan samun saƙonnin da ke tuna mata abin da ya faru gare ta, kuma shirin da ake yi na rufe ma’aikatar ya ɗaga mata hankali.
”Bai kamata a rufe wannan ma’aikata ba, tana da muhimmanci, tana taimaka wa waɗanda suka samu kansu cikin irin halin da na tsinci kaina.”
Asalin hoton, others
Wata da watanni ina son tattaunawa da shugaban ma’aikatar daidaiton jinsi, Kim Hyun-suka, amma gwamnati ta ƙi amincewa da hakan. Daga bisani na tunkare ta a wurin wani taro da na gan ta, na kuma tambaye ta ko ta amince da kalaman shugaban ƙasa da ya ce tsarin cin zarafin mata ya kau?
Sai ta ce ta amince ba a yin hakan a Koriya ta Kudu.
“Ana buƙatar ƙara zage damtse don bai wa mata murya a ma’aikatun gwamnati saboda cike giɓin da ke tsakaninsu, musamman a wuraren aiki,” ta shaida min haka, ba tare da ta amsa tambayar da na yi mata a kan cin zarafin mata ba.
Mun sauya sunan Yuna saboda dalilai na tsaro
Akwai wani ƙarin rahoton da wakilanmu Won-jung Bae suka aiko Hosu Lee