Shugaba Buhari Na Daf Da Sauka Daga Mukamin babban Ministan Man Fetur


buhari-3

 

 

Rahotannin dake ishe mu ta karkashin kasa na nuni da cewar akwai yiwuwar shugaba Buhari ya ajiye mukaminsa na babban ministan man fetur domin samun damar fuskantar matsalolin da ke addabar Nijeriya a natse musamman karayar tattalin arziki.

Majiyar ta tsegunta mana cewar ana zaton Shugaba Buharin zai mika wannan matsayi ne ga gwamnan jihar Edo Adams Oshomole a watan Disamba na wannan shekarar bayan Oshomolen ya mika ragamar mulkin jihar ta Edo ga sabon zababben gwamnan jihar Mr.Godwin Obaseki.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like