Shugaba Buhari Na Hannun Kwararrun Likitoci A Turai – Lai MuhammadGwamnatin tarayya ta tabbatarwa ‘yan Najeriya da cewa, Shugaba Muhammadu Buhari na hannun kwararru likitoci wadanda suka san makamar aikin su a birnin London inda ya je a duba lafiyar jikin sa.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bada wannan tabbaccin a yau Laraba 31 ga watan Mayu 2017 a lokacin da ya ke ganawa da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa bayan zaman majalisar zartarwa na kasa wanda mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo ya jagoranta.

Ministan yayi wannan bayanin ne a yayin da yake amsa wata tambaya a kan matsayin lafiyar shugaban.Ya kuma tabbatar da cewa babu wani damuwa game da rashin lafiyar shugaban kasa.

Shugaban kasa na hannun kwararru likitoci wadanda suka san makamar aikin su babu wani abun damuwa,’ ministan ya ce.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like