Shugaba Buhari Ne Zai Lashe Zaben 2019 – Fadar Shugaban KasaMai taimakawa Shugaba Buhari kan harkokin manema labarai, Malam Garba Shehu, yace ko da a yau aka gudanar da zaben shugaban kasa, toh lallai Buhari ne zai lashe zaben, domin a cewarsa, ‘yan Najeriya na farin ciki da yadda salon mulkin Buharin yake. 
Mal Garba Ya  fadi hakan ne a gaban manema labarai. Malam Garba Shehun, ya kara da cewa, ai ma duk soki-burutsu ne na siyasa jam’iyyar adawa take yi, domin kayen da suka sha a shekaru biyu da suka gabata a shekarar 2015.
An dai shafe shekaru biyu kenan tun da jam’iyyar APC ta amshi mulki, kuma shugaba Buhari na jinya a asibiti a Turai, kusan duk tsawon wannan shekara, bai kuma cewa zai yi takara ko bazai yi takara ba a zabe mai zuwa.

You may also like