Shugaba Buhari Ya Bai Wa EFCC Umarni Da Su Fadada Bincikensu Har Kan Iyalinsa


 

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa ta kasar (EFCC) da ta fadada bincikenta har zuwa ahalin gidansa (‘iyalinsa da ‘ya’yansa) da ake zargi da hannunsu a wata harkala ta cin hanci

Shugaban ya bayyana cewa ba zai yafe wa hukumar ba in har ta ki bincikar tare da kwamushe ko ma waye daga ahalinsa da hukumar ta samu da hannu a wata badakala ta cin hanci da rashawa.

Littafin da aka kaddamar a kwanakin baya akan shugaba Buhari da wani bature mai suna Farfesa John Paden ya rubuta akan rayuwa, ayyuka da kalubalen shugabanci na Muhammadu Buhari wanda sunan littafin ya ke: “Muhammadu buhari: The challenge Of Leadership in Nigeria” ya bayyana manhajar da Buhari zai yi amfani da ita wajen yakar cin hanci da rashawa a Nijeriya.

Littafin har ila yau ya bayyana yadda Shugaba Buhari ya zaburar da shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu wajen koyon hikimar yaki da almundahana a lokacin yana dan makaranta

Littafin ya kuma bayyana bukatar shugaba Buhari na kokarin kawo gyara a bangaren shari’a a matsayin manyan abubuwan da ya ke so ya cimma

Dama dai Buhari ya dade yana fadawa masu ruwa da tsaki a harkar yaki da cin hanci da rashawa cewa ba zai yafe musu ba matukar suka ki bincikar iyalinsa in har aka samesu da wata badakala

 

 

 

Daga: Alummata

You may also like