Shugaba Buhari Ya Bayyana Ranar Da Bazai Taba Mantawa Da Ita Ba A Rayuwarsa


Shugaba Muhammad Buhari ya sake jaddada cewa ba zai taba manta ranar da Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya kira shi a waya don ya taya shi murnar lashe zaben 2015.

Buhari ya ce Jonathan ya bugo wayar ce da misalin Karfe biyar da kwata na Yamma wanda a lokacin sai da shi kansa ya fita cikin gayyaci sa na wani lokaci. Ya ce Jonathan ya shaida masa cewa shi kadai ne dan siyasar da ya tafi har matakin kotun koli sau uku don kalubalantar sakamakon zabe amma duk haka ban yi guiwa kasa ba kan cimma manufata na zama Shugaban kasa.

Buhari ya kara da cewa a lokacin Jonathan na da dukkan makamin da zai iya janyo rigima na kin amincewa da sakamakon zaben amma kuma ya nuna dattako wajen amincewa da sakamakon, don haka ne, a cewar Shugaban ba zai taba mantawa da wannan ranar ba.

You may also like