Shugaba Buhari Ya Bayyana Sirrin Samun Lafiyar Sa



Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana cewa tun bayan da ya dawo jinya daga kasar waje yake ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya saboda cin abinci sosai da kuma yin barci isasshe da yake yi.

Buhari ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da Ministan Abuja ya jagoranci wata tawaga wadda suka kai masa gaisuwar Kirismeti inda ya tabbatar da cewa yana bin umarnin da likitoci suka ba shi na yin barci isasshe da cin abinci sosai inda ya ce, da na dauka Shekaruna 74 Amma Ka Ce Na Kai 75.

You may also like