Shugaba Buhari Ya Buƙaci Majalisar Zartarwa Ta Ƙasa Da Su Ƙyale Shi Ya Huta


muhammadu-buhari2

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙauracewa zaman majalisar zartarwa ta ƙasa data sabayi a kowacce Larabar mako, inda ya buƙaci mambobin majalisar da su ƙyaleshi ya huta.

Zaman majalisar na yau, ya ɗauki tsawon sa’a guda da mintuna arba’in, ya kuma samu jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo.

Bayan taron ministan yaɗa labari Alhaji Lai Muhammad ya faɗawa ƴan jaridu masu ɗauko rahoto daga fadar shugaban ƙasa cewa, shugaban ƙasa ya buƙaci ƴan majalisar zartarwar da su ƙyale shi ya huta.

Ministan yace shugabn ya zaɓi ya riƙa aiki daga gidansa, shugaba Buhari ya nemi da akai masa dukkanin wasu fayal na aikin ofishinsa zuwa gida.

Muhammad ya ƙara da cewa nan gaba mataimakin shugaban ƙasa zai ziyarci Buhari a gidansa.

“Yanzu yanzu muka kammala zaman majalisar zartarwa ta ƙasa, na tabbata kun lura da cewa shugaban ƙasa bai kasance tare damu ba, bai kasance tare damu ba saboda ya buƙaci da a bashi hutu inda ya nemi mataimakinsa da ya jagoranci zaman na yau”

 

 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like