A safiyar yau, Shugaba Muhammadu Buhari da tawagar Nigeria suka gana da Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel, a Chancellery a birnin Berlin.
Shugaba Buhari a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa ganawar na da matukar muhimmanci kuma ta fi maida hankali ne kan tsaro, tattalin arziki da karfafa dangantaka tsakanin Nigeria da Jamus.