Shugaba Buhari ya gana da ‘yan matan Chibok


 

 

Gwamnatin Najeriya ta gudanar a wannan Laraba a birnin Abuja da bikin karbar ‘yan matan Chibok 21 da Boko Haram ta sako, a karkashin jagorancin Shugaba Buhari

Nigeria 21 Chibok-Mädchen (Picture-Alliance/dpa/EPA/STR)

Gwamnatin Tarrayar Najeriya ta ce ta dauki nauyin rayuwa da daukacin ilimi da aiyyukan ‘yan mata ‘yan makaranta na Chibok 21 da kasar ta karbo daga Kungiyar Boko ta Haram a cikin makon jiya. Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ne ya sanar da hakan a lokacin bikin karbar ‘yan matan na Chibok a wannan Laraba a Abuja.
A karkashin jagorancin rebecca malum ‘yan matan na Chibok sun rika rera waka ta godiya ga gwamnatin kasar da suke kallo a cikin kimar gaske bayan sakin da yai kama da mafarki cikin kasar a halin yanzu.
sama da kwanaki 900 ne dai ‘yan matan sama da 200 suka share a cikin dokar daji a hannun Kungiyar ta Boko Haram. Duk da cewar dai sun iso birnin na Abuja a cikin yanayi maras kyau, bayan share tsawon mako guda sun fara nuna alamun sauyawa sakamakon matakan kula da lafiya da kuma shawarwari na rayuwa.

Nigeria Chibok Heimkehr Entführte Mädchen (picture-alliance/AP Photo/O. Gbemiga)

To sai dai kuma bayan ganin bakin na kwana da yawa, daga dukkan alamu kuma tana shirin sauyawa a bangaren ‘yan matan da gwamnatin kasar ta ce ta dau nauyin komai nasu har zamansu mutane masu hankali a fadar shugaban kasar da ta karbe su:

“Ko bayan cetonsu za mu kuma dauki nauyin kula da su da iliminsu da rayuwarsu da ke gaba. Tabbas ba á makara ba ga ‘yan matan na komawa makaranta domin cigaba da karatu. Wadannnan ‘ya’ya namu sun ga baki cikin da duniya ke iya bayarwa, yanzu lokaci ne a garesu da za su ga farin ciki na duniyar Allahu“

karatun kuma da ya burge iyayen ‘yan matan dama ragowar shugabannin al’umma na Chibok din a fadar Mr Yakubu Kinke da ke zaman shugaban kungiyar iyayen ‘yan matan.

Nigeria Chibok Heimkehr Entführte Mädchen (picture-alliance/AP Photo/O. Gbemiga)

To sai dai koma menene fatan ‘yan mata da iyayen nasu dai daga dukkan alamu hasken da ya kai ga sakin ‘yan matan ya fara alamun komawa ga duhu sakamakon sabbin hare-hare daga ‘ya’yan Kungiyar ta Boko Haram a cikin yankin Borno.
To sai dai kuma a fadar Janar Mansur Dan Ali mai ritaya da ke zaman ministan tsaron kasar,ba bu tada hankali a cikin abun da ke sake faruwa cikin yankin yanzu:

“Tunda ya yi alkawari ‘yan matan nan za su yi makaranta, bukatarmu ta kare. Kuma za a kula da lafiyarsu , abin da muke so kenan dan haka mun ji dadi mu gode wa shugaban kasa da ya dauki wannan mataki ba tare da mun roke shi ba”

Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba a bangare na gwamnatin da ke fatan kare yakin na ta’addanci a cikin sauri da kuma ke kallon kafa cikin sakin ‘yan matan.

You may also like