Shugaba Buhari Ya Gana Da Zababben Shugaban Kasar Ghana Akufo-Addo A Abuja


 

 

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya gana da shugaban kasar Ghana mai jiran gado Nana Akufo-Addo a birnin Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriyar inda suka tattauna kan batutuwa daban-daban.

Kafar watsa labaran nan ta Premium Times da ke watsa labaranta ta hanyar internet ta ce shugaba Buharin ya gana da zababben shugaban na Ghana ne wanda ya kawo ziyara Nijeriya a asirce ba tare da an yi cikakken bayanin dalilin ganawar ba.

Jim kadan bayan gama ganawar, Mr. Akufo-Addo ya gana da manema labarai a fadar mulkin ta Nijeriya inda ya bayyana cewar yana fatar alakar da ke tsakanin Nijeriya da Ghana za ta kara karfafuwa a lokacin shugabancinsa.

Zababben shugaban kasar Ghanan ya kara da cewa ya zo Nijeriya din ne a wata ziyara ta kashin kansa inda ya halarci wani taro da aka gudanar a birnin Lagos dangane da makomar nahiyar Afirka; sai dai ya ce ganawar tasa da shugaba Buhari ta yi kyau sosai inda ya ce yayi amfani da wannan damar wajen bayyana wa shugaba Buhari shi wane ne sannan kuma ta taya shugaban Nijeriyan murnar cikarsa shekaru 74 a duniya.

A ranar 7 ga watan Janairu mai kamawa ne Mr. Akufo Addo zai karbi ragamar mulkin kasar Ghanan bayan ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a kwanakin bayan inda ya kayar da shugaba mai ci John Dramani Mahama.

You may also like